MATAKIN DAYAKAMATA KA DAUKA WAJEN KARE KANKA DAGA SHARIN MASU SATAR KUDI A BANKI
Assalamu Alaikum . yau InshaAllah zamuyi magana akan wata matsala da tazama ruwan dare acikin al'umma, a wannan zamani akwai wasu batagari masu amfani da wasu hanyoyi wajen sacewa mutane kudade a akaunt din su , kawai kana zaune saikaji debit alert wanda bakasan dashi ba, kuma inkaje banki sai suce da kai kaine ka ciri kudin saboda da layinka akai amfani aka cire kudin. akwai hanyoyi dayawa dasu wadannan bata gari suke bi wajen satar bayanai daga jamaa wanda mutane da dama basa kulawa ko damuwa da mahimmancin waddannan bayanai . sudai waddan mutane kulum acikin bincike suke akan yadda zasu cutar da alumma, su sun kasance suna bacci da rana da da daddarekuma sai su hau Internet suyi ta gwada sa'arsu har su dace. kadan daga cikin bayanai dasuke sata sun hada da. 1. shekarun haihuwar wanda zasu iya samu a facebook dinka ko wata social media zama su iya kiranka awaya su yaudareka da cewa su ma'aikatan bankine suna so san wasu bayanai agurinka wanda idan kai kuskure ka fa...