KANA BUKATAR KOYAN ILIMIN COMPUTER DA YANAR GIZO
Assalamu Alaikum YAN NAJERIYA GA DAMA DAGA PANTAMI Maigirma Ministan Sadarwa da Tattalin arziki ya kaddamar da manhajar yanar gizo da ta wayar hannu, ga yan Najeriya domin samun garabasa wajen koyan sana'o'i iri-iri na zamani, da samun guraren aiyukan yi cikin sauki, kuma an tsarashi yadda zaka koya da kanka tahanyar bidiyo da rubutu, wannan tsarin yanada matukar mahimmanci da kuma amfani sosai ga al'ummar Najeriya. Wannan tsari yanada saukin fahimta da kuma saukin amfani ga mai aiki da shi, sannan ba sai kana da data a wayar ka ko Computer kaba zaka iya shiga tsarin, tsarin ankasa shi kashi uku ne akwai #Digital_Nigeria akwai #NITDA_Academy da kuma #IBM_Digital_for_Africa, ko wanne yana da mahimmanci kuma za'abaka certificate bayan kammala training din. Ga yadda tsarin ko wanne yake da yadda za'ayi amfani da manhajan da kuma amfaninsu ga yan Najeriya. #DIGITAL_NIGERIA Shi wannan tsarin yana da tsarurruka da yawa a kasa dashi, zaka koyi sa...