MATAKIN DAYAKAMATA KA DAUKA WAJEN KARE KANKA DAGA SHARIN MASU SATAR KUDI A BANKI
Assalamu Alaikum.
yau InshaAllah zamuyi magana akan wata matsala da tazama ruwan dare acikin al'umma, a wannan zamani akwai wasu batagari masu amfani da wasu hanyoyi wajen sacewa mutane kudade a akaunt din su , kawai kana zaune saikaji debit alert wanda bakasan dashi ba, kuma inkaje banki sai suce da kai kaine ka ciri kudin saboda da layinka akai amfani aka cire kudin.
akwai hanyoyi dayawa dasu wadannan bata gari suke bi wajen satar bayanai daga jamaa wanda mutane da dama basa kulawa ko damuwa da mahimmancin waddannan bayanai .
sudai waddan mutane kulum acikin bincike suke akan yadda zasu cutar da alumma, su sun kasance suna bacci da rana da da daddarekuma sai su hau Internet suyi ta gwada sa'arsu har su dace.
kadan daga cikin bayanai dasuke sata sun hada da.
1. shekarun haihuwar wanda zasu iya samu a facebook dinka ko wata social media
zama su iya kiranka awaya su yaudareka da cewa su ma'aikatan bankine suna so san wasu bayanai agurinka wanda idan kai kuskure ka fada musu zasu yi amfani dasu wajen cutar dakai. kuma bankuna suna ta sanar da jamma cewar basa kiran kostoma yabasu wani bayanai sai dai yaje banki.
2. lambar wayarka/layin wayarka zasu iya satar wayarka ko suyi swaping dinka idan sukasan cewar anai maka alert da wannan layi.
3. sanin lambobin sirin ka na ATM zasu iya bibiyarka har inda kake cire kudi kuma su leka suga lambobin sirrinka. ko kuma su sace maka ATM.
matakan daya kamata ka dauka
1. dena amfani da layin da akemaka alert a social medias.
2. indan wayarka ta fadi ko aka sace kuma layin da yake kai dashi akemaka alert sai ka dau matakin gaggawa kasanar da bankinka kafin ai maka aika aika.
3. idan kaje ATM kaga wani yana kokarin lekaka to ka tareshi idan kuma kaga ya biyoka to kai sauri ka sannar da jamian tsaro.
akwai hanyoyi dayawa aman zamu tsaya a nan sai wani lokaci.
mungode.
Tambayata anan itace ta Yaya zanyi in boye lambar wayata a Facebook batareda mutani sun ganiba?
ReplyDelete