Posts

Showing posts from April 11, 2021

MATAKIN DA YADACE KA DAUKA IDAN AN SACE MAKA WAYA KO KUMAKAGA ANA CIRE MAKA KUDADE A ASUSUN AJIYARKA NA BANKI.

Image
Assalamu alaikum. Barkanmu dasake saduwa a wannan shafi mai albarka,  yau InshaAllah zamuyi takai taccen bayani akan matakan da ya kamata ka dauka don tsare kanka daga sharin masu sacewa jamaa kudade a asusun ajiyar su na banki. Kasancewar yanzu kwacen wayar hannu yazama ruwandare a kullum sai kaji wani yace an tare shi  an kwace masa waya ko kuma an sace,  wanda kuma daga baya sai wanda ya saci wayar yayi amfani da layin kan wayar ya sace wa mai wayar kudaden sa acikin bankinsa na ajiya. Yanada kyau kafin a sace maka waya ka tabbata ka sakawa layin wayarka lambobin tsaron tayadda koda ansace wayar baza a iya amfani da layinba wajen yi maka sata a asusun ajiyarka. Bincike ya nuna mafiyawan kwacen wayoyin hannu da akeyi yanzu anayi ne don a samu damar yin amfani da layin kan wayar don sacewa mai wayar kudadensa a asusun ajiyarsa na Banki. Wannan matsalar tafaru da dubban mutane wadanda bayan an sace musu waya anyi amfani da layin su wajen sace musu kudade a asusun ajiyar s...