KANA BUKATAR KOYAN ILIMIN COMPUTER DA YANAR GIZO
Assalamu Alaikum
YAN NAJERIYA GA DAMA DAGA PANTAMI
Maigirma Ministan Sadarwa da Tattalin arziki ya kaddamar da manhajar yanar gizo da ta wayar hannu, ga yan Najeriya domin samun garabasa wajen koyan sana'o'i iri-iri na zamani, da samun guraren aiyukan yi cikin sauki, kuma an tsarashi yadda zaka koya da kanka tahanyar bidiyo da rubutu, wannan tsarin yanada matukar mahimmanci da kuma amfani sosai ga al'ummar Najeriya.
Wannan tsari yanada saukin fahimta da kuma saukin amfani ga mai aiki da shi, sannan ba sai kana da data a wayar ka ko Computer kaba zaka iya shiga tsarin, tsarin ankasa shi kashi uku ne akwai
#Digital_Nigeria akwai
#NITDA_Academy da kuma #IBM_Digital_for_Africa, ko wanne yana da mahimmanci kuma za'abaka certificate bayan kammala training din. Ga yadda tsarin ko wanne yake da yadda za'ayi amfani da manhajan da kuma amfaninsu ga yan Najeriya.
#DIGITAL_NIGERIA
Shi wannan tsarin yana da tsarurruka da yawa a kasa dashi, zaka koyi sanin menene computer da yadda ake sarrafata da kuma sanin manhajoji da computer ke dauke dasu, sannan ta yaya zaka sarrafasu kanemi kudi dasu. Misali akwai tsari na masu koyo wanda basusan computer ba kamar haka;
#DIGITAL_SKILLS
1. yadda zakayi aiki da computer,
2. yadda zaka samu bayanai ta yanar gizo
3. yadda zaka bayar da kuma yada bayanai ta yanar gizo
4. yadda zaka kiyaye kanka sharrin yandamfara a yanar gizo
5. Yadda zaka kir-kiri wani abu da computer
6. yadda zaka kula da manhajarka a computer
7. Yadda zakayi ammani da manhajar Microsoft office
Sannan akwai tsari na wadanda sunfara koyon computer, da sanin yanar gizo tsarinsu yananan kamar haka;
#INTERMIDIATE_DIGITAL_SKILLS
1. yadda zakayi manhajar computer
2. yadda zakayi manhajan computer da HTML da CSS
3.Yadda zakayi manhaja mai nazari da kanshi
4.Yadda zakayi ammani java script
5.Yadda zaka kir-kiri Manhaja
Da kuma tsarin wadanda sukayi nisa da sanin computer da yanar gizo harma da kirkire-kirkiren manhaja da computer, suma ga tsarin su kamar haka;
#ADVANCE_DIGITAL_SKILLS
1. yadda zakayi amfani da Data science analytical
2. yafda zakayi ammani da HTMAL 5
3. yadda zakayi ammani da node.Js
4. yadda zaka koyi Netwoking
5. yadda zaka koyi kir-kiran manhajar computer da na wayar hannu
6. yadda zaka koyi aiki daduk wani nau'i na computer da manhajarsa.
7. Yadda zakayi kasuwa da comuter ta hanyar yanar gizo
8. yadda zaka tallata kasuwar ka ta hanyar yanar gizo
9. yadda zaka nemi masu sayan kayan ka ta hayar yanar gizo
10. yadda zaka bada gudumawa a gwamnati ta yanar gizo
11. yadda zaka dauki ma aikatanka ta hayat yanar kizo
12. yadda zaka nemi aiki ta hayar yanar gizo
#NITDA_ACADEMY
ita kuma wannan tanada tsari kashi uku wanda masu bangaren zasu amfana dasu, kamar haka;
1. MDAs training yanada courses nashi da dama.
2. students Training yanada courses nashi da dama dasuka shafi yan makaranta
3. General training wannan ta shafi kowa da kowa
#IBM_DIGITAL_FOR_AFRICA
Wannan tsarine da Kamfanin Amurka ke koyarwa domin fahimta manhajar zamani a Afrika suma gasu kamar haka;
1. yadda zaka koyi yin manhaja da artificia intelligent
2. yadda zaka koyi yin manhaja da data science
3. yadda zaka koyi yin manhaja da internet of things
4. yadda zaka koyi yin manhaja da machine lerning
5. yadda zaka koyi yin manhaja da blockchain
6. yadda zaka koyi yin manhaja ta hayar github
#Amfaninsa_ga_yan_Najeriya
1. samun ilimin computer kyauta
2. samun aikinyi cikin sauki
3. koyon sana' o'in Zamani cikin sauki kyata
4. sanin surrun 'yan damfara (yahoo boys)
5. yin arziki cikin sauki da sauri
6. samar da kudin shiga wa kada
7. bungasa tattalin arzikin kasa
8. rage aiyukan ta'addanchi
Sannan ina so ku fahimci cewar ko wane tsari yana da 'ya'ya a kasa da shi, sannan kuma in kuka gama ko wace tsari za'a baku certificate
domin shiga tsarin danna wannan bulun rubutun https://www.digitalnigeria.gov.ng please kuyi share saboda wasuma su gani su amfana dashi. Nagode
Muhammad Hardo Bello
National Coordinator Pantami Care foundation
Follow us on Telegram
Wannan abu yayi dari bisa dari
ReplyDeleteNayi matukar jindadi da wannan abun alkhairi
ReplyDeleteYayi kyau
ReplyDelete