MATAKIN DA YADACE KA DAUKA IDAN AN SACE MAKA WAYA KO KUMAKAGA ANA CIRE MAKA KUDADE A ASUSUN AJIYARKA NA BANKI.

Assalamu alaikum.
Barkanmu dasake saduwa a wannan shafi mai albarka,  yau InshaAllah zamuyi takai taccen bayani akan matakan da ya kamata ka dauka don tsare kanka daga sharin masu sacewa jamaa kudade a asusun ajiyar su na banki.
Kasancewar yanzu kwacen wayar hannu yazama ruwandare a kullum sai kaji wani yace an tare shi  an kwace masa waya ko kuma an sace,  wanda kuma daga baya sai wanda ya saci wayar yayi amfani da layin kan wayar ya sace wa mai wayar kudaden sa acikin bankinsa na ajiya.
Yanada kyau kafin a sace maka waya ka tabbata ka sakawa layin wayarka lambobin tsaron tayadda koda ansace wayar baza a iya amfani da layinba wajen yi maka sata a asusun ajiyarka.
Bincike ya nuna mafiyawan kwacen wayoyin hannu da akeyi yanzu anayi ne don a samu damar yin amfani da layin kan wayar don sacewa mai wayar kudadensa a asusun ajiyarsa na Banki.
Wannan matsalar tafaru da dubban mutane wadanda bayan an sace musu waya anyi amfani da layin su wajen sace musu kudade a asusun ajiyar su na banki.
Don haka yana da kyau kowa ya dauki matakin gaggawa akan wannan matsala.


1. YADDA ZAKA SAKAWA LAYINKA LAMBOBIN TSARO.
Dafarko dai ka shiga setting na wayarka ta android,  sai ka shiga security and location kamar yadda muka nuna awannan hoton 👇
saika shiga SIM card luck kamar yadda yake a wannan hoton 👇
saikai activating din luck din kamar yadda yake a wannan hoton na kasa, idan kai activating din SIM lock zasu tambayeka pin sai ka saka 00000 ziro guda 5 shine default pin dinka, daga nan kuma sai ka canja pin din sai kasaka wani pin din da kai kadai kasani.
Idan ka sakawa SIM dinka tsaro koda an sace maka waya baza a iya yin amfani da layinba wajen sace maka kudade a banki,  saboda duk lokacin da aka kashe wayar aka kuna layin bazai hau Network ba sai an saka wannan pin din da ka kirkira.

YADDA ZAKA DAKATAR DA CIRE KUDI  A ASUSUN AJIYARKA NA BANKI BAYAN AN SACE MAKA WAYA
idan ka manta baka sakawa layinka lambobin tsaroba kuma gashi an sace maka waya,  ko kuma ba a sace  wayarba amman kawai sai kaji ana kwashemaka kudade a asusun ajiyarka na banki sai kai sauri ka dannna waddannan lambobi *966*911# akan kowace waya kasamu idan ka danna zasu tambayeka Account number dinka bayan kasaka sai ka dakatar da cire kudi daga account dinka,  tayadda babu wanda zai iya cire kudi a Account din ko kaima sai kaje Bank kafin su sake activting din Account din don gudanar da hadahadar kudade.
Don Allah Jama'a a taimaka ayi sharing. 
Wassalam. 
Zaku iya bibiyar mu a Telegram 

Comments

Popular posts from this blog

YADDA ZAKA SAI KATI KO TURA KUDI DAGA BANK ACCOUNT DINKA

YADDA ZAKAYI TARaNSFAR DATA DAGA LAYINKA ZUWA WANI LAYI

YADDA ZAKA DAWO DA FACEBOOK ACCOUNT DINKA DA AKA KWACE