YADDA YAZAKA TSARE FACEBOOK ACCOUNT DINKA

Assalamu Alaikum.

Dafatan anyi sallah lafia dafatan Allah ya karbi ibadunmu ya yafe mana kurakuranmu yasa mu a cikin yantattu Amin.

Yau inshaAllahu zanyi magana akan hanyoyin da zakabi wajen tsare Facebook Account dinka daga sharrin masu satarbayanai tahanyar kafofin sadarwa na social medias.
Kasancewar Facebook mafi shahara wasu bata gari suna amfani dashi wajen satar bayanai don yin amfanin dasu wajen cutar awani kokuma su yi amfani da Account din wani dan su yaudiri jamaa wanda akarshe suke damfarar wasu jamaa ta tahanyar BASAJA da sunan wani . Missali akwai maza dayawa da suke amfani da Account na mata don yaudar maza wanda akarshe suke yaudarar jamaa harma su damfare su.

Wasu kuma sukan bude Account dasunan wasu manyan shwagabani ko manyan jamian tsaro na kwastam suna talan kayan GWANJO na kwastam wanda akarshe suke damfarar jamaa.

Wasu kuma suna kwace Facebook Account din jamaa ne wato "hacking" wanda akarshe sukeyin BASAJA don su cutar da abokan mai wannan Account din.

Wasu kuma idan sukayi hacking din Account din jamaa sai suyi ta posting hotuna batsa.

Akwai hanyoyi dadama da wadannan azaluman suke bi wajen cutar da jamaa.

Hanyoyin da zaka bi dan tsare Facebook Account dinka .

1. Boye numbar wayarka akan Facebook Account dinka.

2. Boye email dinka akan Facebook Account dinka.

3. Boye shekarun haihuwa akan Facebook Account dinka.

4. Yin amfani da step 2 verification wato idan wani yayi kokarin login Account dinka zaayimaka text cewar wani yanason ya shiga Account.kokuma duk lokacinda zakayi login a Account dinka sai  turo maka da code wasu nambobi sannan kayi login.

5. Karka sanar da kowa lambobin sirinka

6. Trusted contact  wato zabar mutane 5 daga cikin abokanka dazasu iya temakamaka wajen kwato Account dinka idan ansami matsala. E.t.c

Akwai hanyoyi da dama aman wadannan sune mafi mahimanci kuma indai kabi wadannan matakai babu wanda ya isa ya kwace maka Facebook Account komai sharinsa komai fasaharsa saidai yayi hakuri.

Zaka iya amfani da abun da nafada a sama tahanyar shiga Facebook Account dinka saika shiga setting sai kashiga Privacy setting kawai sai ka boye nambar wayarka, Email dinka da shekarun haihuwa tayadda bawanda zai iya gani saikai.
Dafatatan Allah yasa mudace.
Nagode.

Eid-Mubarak

Comments

Popular posts from this blog

YADDA ZAKA SAI KATI KO TURA KUDI DAGA BANK ACCOUNT DINKA

YADDA ZAKAYI TARaNSFAR DATA DAGA LAYINKA ZUWA WANI LAYI

YADDA ZAKA DAWO DA FACEBOOK ACCOUNT DINKA DA AKA KWACE