ABUBUWAN DA KE JAWOWA A KWACE MAKA FACE BOOK ACCOUNT, EMAIL, DASAURANSU

ASSALAMU ALAIKUM.
🌟   ★    ⭐    ⭐  ☆

barkanmu da sake haduwa a wannan dandali nine naku Muhammad  Auwal Aliyu ayau InshaAllah kamar yadda muka saba yau zanyi magana akan dalilan da suke sawa wasu batagari a yanar gizo suke kwacewa mutane Facebook, Email da sauransu dan satar bayanai wanda akarshe suke cutar da jamaa tahanyar kwace wa da kuma satar bayain.

bayan dogon nazari da bincike, bincike ya nuna cewar mafiyawan dalilan sun samo asaline daga yin amfani da lambobin siri masu saukin ganowa.
missali kaso 30% na masu amfani da yanar gizu suna amfani da shekarun haihuwa amatsayin lambobin tsaro.

haka zalika bincike yanuna kaso 15% suna hada sunansu da shekarun haihuwar su.

kaso 10 suna amfani da lambobi masu saukin kamar  12345678

kaso 10% suna amfani da lambar wayarsu ko wani yanki amatsayin lambobin tsaro

kaso goma suma amfani da sunayen yayansu ko masoyansu amatsayin lambobin tsaro.

kaso 40% kawai suke amfani da lambobin tsaro masu wuyar ganowa.

haka zalika masu amfani da ATM ko mobile bank  kaso 45% sukanyi amfani da shekarun haihuwa ko wani yanki na lambar wayarsu,  ko kuma lambobi kamar 1234.

idan dai kana cikin masu amfani da wadancan lambobin siri kamar yadda na zayyana asama kayi gaggawar canja lambobin sirinka (Password ) tun kafin ka fada hannun wadannan bata gari.

bayan nazari da laakari da wadancan matsalolin anfitar da tsari makamar haka .
1. yin amfani da lambobin tsaro masu wuyar ganowa .

2. hada kalma da lamba da kuma
alamar rubutu missali Kano01!? ko ? !01kano.

3. yin amfani da sunnan abunda baza a taba predicting ba missali peace& unity, shinkafa dawake,  furada nono e.t.c

4. daina amfani da shekarun haihuwa amatsayin lambar zaro .

5. daina amfani da lambar waya ko wani yanki nata amatsayin lambar tsaro.

6,daina amfani dasunan ka batare da kahadashi da lambobiba ko alamar rubutu.
da sauransu.

note.
kwanaki nayi makamancin irin wannan post din aman ansamu wasu daga cikin waddan batara gari sun turomin da sakwanni ta email marasa dadi to nidai bazan daina tonamuku asiriba matukar ina raye.

⭐           ★         ☆             🌟
dafatan Allah yasa mudace
nagode.

Comments

Popular posts from this blog

YADDA ZAKA SAI KATI KO TURA KUDI DAGA BANK ACCOUNT DINKA

YADDA ZAKAYI TARaNSFAR DATA DAGA LAYINKA ZUWA WANI LAYI

YADDA ZAKA DAWO DA FACEBOOK ACCOUNT DINKA DA AKA KWACE