FASAHAR KERE-KEREN WAYAR HANNU
FASAHAR KERE KERE. |
Assalamu alaikum,
Yau InshaAllah zamuyi tsokaci akan fasahar kere-kere. Kasancewar mu ma'abota amfani da wayar hannu, computer da makamantansu, yana dakyau mu kasance masu nazartar tare da zurfafa tunani akan waddannan abu buwa kamar haka.
1. Ya ake kera wayar yannu.
2. Yaushe aka fara kirkiri waya
3. Waye ya kirkiri waya
Da sauransu.
Babbar matsalar mu a yankin Africa shine rashin zurfafa bincike akan irin wadancan abubuwa, sannan kuma gwamnatocinmu basa tallafawa harkar kerekere zaka iya samun yara da yawa wadanda suna da basira matuka aman gwamnatocin mu basa damuwa da irin waddan nan matasa, sunfiso a kodayaushe muzamo cima zaune saide a kera mana mu saya, wanan dalilin ne ma yasa zakaga kullum turawa saide su kiramana kaya mu siya.
Idan ka dauki waya kadai zakaga kudin da kamfanoni wayoyin nan suke samu sunfi kudin da ake samu a manfetir a Nigeria.
Kulum sai wani kamfani yafito da sabuwar waya mukuma sai gasar siya muka iya, kulum burin mu mu rike wayar da babu wanda yake da irinta komai tsadarta,
Aman bamu damu da yin tuna ni akan yaya akeyin koda batirin wayane, ko mic ko sensor, bama tunanin taya zamu yi muma mu kera wayar da kanmu.
Yanada kyau musani cewar, turawan dasuke kere-kere ba finmu sukayiba suma mutane ne kamar mu, kawai jajircewar su da bincikensu ne yafi namu, idan muka jajirce tare da zurfafa bincike, tabbas zamu iya kera kayan dayafi nasu.
To aman babbar matsalarmu daga Gwamnatine babu wani tanadi da akayi akan hakan don tallafawa yara masu hazaka.
Yana da kyau Gwamnatoci su duba wannan matsala don kawo sauyi a harkar kimiya da fasaha.
Mungode.
InshaAllah zamu ci gaba wani lokaci,
Zamu yi bayani akan yadda aka kirkiri wayar hann.
Zaku iya bibiyar shirye shiryen mu whatspp
Ko facebook
Zaku iya turo da tambayoyinko ko ra ayoyinku
ta email. duniyarwaya7@gmail.com
Comments
Post a Comment
Thank you for your comment