YADDA ZAKA MAGANCE MATSALAR BATTAN TAKADDUN KA

Assalamu Alaikum.
Barkanmu dasake saduwa a wannan dandali,  yau InshaAllah zamuyi bayani akan hanyoyin dazakabi don magance matsalar batan takaddun makarantar ka ko kuma wasu takaddu masu mahimmamci a rayuwar mu tayau da kullum.

Kasancewar dan adam yanada mantuwa, wanilokaci sai ka ajiye abu kuma ka manta a inda ka ajiye,  ta iyayiwuwa kuma lokacin da bugatar abun zata taso sai ka manta a ina ka ajiye,  wani lokaci kuma,  ana iya samun matsala ta batan takaddun kokuma ibtilain gobara ko wani abu makamancin hakan.

Wasu lokutan kuma zaka iya yin tafiya don neman aiki ko wani abu makamancin hakan aman sai ka manta da wata takadda da bata taka kara ta karya ba kuma watakila dole se da ita za kasamu abun da kakeso.

Yana da kyau ka bi wadannan hanyo don magance irin wannan mtsala.

1. Ka yi scanning din dukkan takaddunka ka ajiye su a cloud storage (wato ma'ajiya ta yanar gizo) dinka.

2. Duk lokacin da wata takadda mai mahimmaci  tazo hannunka sai kayi kokari kayi scanning dinta kuma kakaita cloud storage dinka.


3. Yanada kyau ace kana da cloud storage fiyeda daya.

4.Yanada kyau ace kakiyaye inda ka ajiye cloud copy dinka don saukin nemowa.

5. Yana da kyau ka ajiye soft copy akan wayarka, saboda koda zaka samu kanka a inda ba network kuma bukatar takaddar ta taso.

Babban abun lura shine duk takaddar da kakai cloud idan ka yi printing dinta zatafita kamar yadda waccan ta ainihi take.



Idan kabi waddancan matakan ka rabu da matsalar batan takadda.

InshaAllah zamu cigaba da bayani akan wanne cloud storage yakamata ka ajiye takaddunka.


Zaku iya bibiyar shiryeshiryen mu a whatspp  don shiga danna nan

Wassalam. 

Comments

Popular posts from this blog

YADDA ZAKA SAI KATI KO TURA KUDI DAGA BANK ACCOUNT DINKA

YADDA ZAKAYI TARaNSFAR DATA DAGA LAYINKA ZUWA WANI LAYI

YADDA ZAKA DAWO DA FACEBOOK ACCOUNT DINKA DA AKA KWACE