YADDA ZAKA SAN ABUNDA YAYANKA SUKEYI AKAN WAYARSU TA WAYARKA

Assalamu Alaikum.

Barkanmu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka,  dafatan muna cikin koshin lafia,  Amin.

Bayan haka yau InshaAllahu zamuyi bayani akan wani tsari da kamfanin  google suka kirkiro wanda ake kira da "google family link"  wannan tsari google sun kirkiro shi do karfafa alaka a dangi ta yadda kowane member na family zai dinga samu bayanai akan yan uwansa wanda ya hada da location, activities, da kuma events.

A wannan tsari google sun ware wani bangare da sukakira da "parental control" wato yadda iyaye zasu dinga kulawa da irin abubuwanda yayansu suke akan wayar su wato smart phones.

Awannan tsari na parental control iyaye za su iya hana yayansa saka  wasu app da basu yadda da suba,  kuma za su iya hana yayansa ziyartar wasu shafikan da basu amince dasuba,  haka zalika iyaye zasu iya sanin dukkan abubuwanda yayansu suke gudanarwa akan wayarsu.
Parental control zai taimaka sosai wajen hana kananan yara ziyartar shafikan da basu da wani amfani.

YADDA ZAKA SAITA PARENTAL CONTROL A KAN WAYAR KA DATA YAYANKA. 

1. Dafarko dai zaka sauke app na google family link akan wayarka a google playstore sai kai installing din app din akan wayarka da ta danka.
2. Sai kai lunching din app din akan wayoyin, idan kai lunching zasu tambayeka email address akan kowane app daka saka a wayoyin. Sai ka saka email din akan apps din,   wato email dinka akan app din daka saka a wayarka, email din danka ko yarka kuma akan app din dakasaka a wayarsa. 

3. Zasu nuna maka wani code akan wayar ka sai ka saka wannan code din akan wayar danka.
4. Bayan ka saka code din zasu nuna maka duk app din da suke kan wayar danka,  sai kai deactivating din duk app din da baka son danka ko yarka yai amfani dashi.

4. Zasu nuna maka yadda zaka kamala saitin. 

ABUN LURA.
Duk wayar da ka dora akan wannan tsarin yaron bazai iya canja wani abu akaiba saida sanin iayaye, kuma koda yayi formatting din wayar bazata karbi duk wani app da akai deactivating akan taba.

GARGADI
kasancewar magidanta da dama naneman hanyar dazasu dinga sanin me matansu sukeyi akan wayoyinsu, wasu zasu iya yin amfani da wannan tsari akan matansu,  to yanada kyau kasani google basu kirkiri wannan tsarin don yin amfani dashi akan matan aureba,  sun kirkireshi ne don kulawa da tarbiyar yara,  don haka duk mijin daya yi amfani da wannan app din akan matarsa to idan kamfanin  google suka ganoshi zasu iya kaishi kara. Dafatan zaa kiyaye.

Mungode.
Wassalam.
Don samun bayanai akan shiryeshiryenmu zaku iya subscribe din wannan shafi, ko kuma kutura da sako zuwa duniyarwaya7@gmail.com
Ko 
ko 

Comments

Popular posts from this blog

YADDA ZAKA SAI KATI KO TURA KUDI DAGA BANK ACCOUNT DINKA

YADDA ZAKAYI TARaNSFAR DATA DAGA LAYINKA ZUWA WANI LAYI

YADDA ZAKA DAWO DA FACEBOOK ACCOUNT DINKA DA AKA KWACE