YADDA ZAKA DUBA LAMBAR KATIN SHEDAR DAN KASAR KA AKAN WAYARKA.
Asalamu Alaikum.
Barkanmu dasake saduwa a wannan shafi mai albarka.
Yau InshaAllahu zamuyi bayani akan National Identity Card wato katin shedar dan kasa.
Kasancewar yanzu kusan duk wani abu dazakayi amatsayinka na dan kasa sai anbukaci shedar katin dan kasa,
Kusan yanzu babu wani abu dazakayi sai an bukaci shedar katin dan kasa, ta kai matakin da ko aiki zaka nema sai ka yi amfani da shedar katin dan kasa, idan zaka bude account a banki , ko zakayi welcome back na layinka da yabata sai ka nuna shedar katin dan kasa.(da sauransu).
Kullum abubuwa cejawa sukeyi, nan gaba kadan ma idan baka da shedar katin dan kasa akwai yiwuwar a ki baka admission a makaranta, ko kuma a hanaka zirga-zirga a fadin kasar nan, don haka yanada kyau kowa yadaure yayi.
YADDA ZAKA DUBA LAMBAR NATIONAL ID DINKA AKAN WAYARKA.
mafiyawan lokaci mutane da dama suna manta lambar katin dan kasar su sakamakon wasu dalilai wani lokacin ma zakaje kayi register aman bazaka samu sleap dinka ba, idan sleap dinka ya bata kuma bakasan yadda zaka samu lambar katin dankasar kaba, kawai ka danna *346# akan wayarka da layin da kai register zaka ga lambar National Identity card dinka ta bayyana sai kai saving dinta da kyau.
YADDA ZAKA SAKE PRINTING DIN SLEAP DIN KA DA KANKA IDAN YA BATA.
Idan sleap dinka na katin dan kasarka ya bata baka da bukatar ka sake zuwa office din National Identity management donsake karbar wani, kawai ka ziyarci google playstore ka sauke wannan app din sai ka saka lambar wayarka da lambar shedar katin dan kasarka zasu bukaci ka zabi pasword don register daga karshe zasu nuna maka sleap dinka sai kayi printing kawai.
GARGADI
Mutane da yawa suna damun kansu akan rashin samun I.card bayan an basu sleap, wanda shi wannan sleap din shine permanent baya expire kuma ko zasu cigaba da amfani dashi koda ba a basu plastic i.dcard ba. Aman shi plastic i.dcard din yana expire bayan shekaru 5 kuma yana daukar shekaru kafin ka samu bayan kayi register, don haka yan uwa indai anbaka sleap dinka ka daure ka adanashi da kyau shine katin shedar dan kasarka.
Wassalam.
Don samun bayanai a email dinku kaitsaye za ku iya suscribing din shafin mu, ko kutura da email zuwa duniyarwaya7@gmail.com.
Ko
Ko
Aslm
ReplyDeleteTo ni nayi National I'd kuma ambani slip amma ya bata kuma number da nai itama ansace wayar name welcome back sunce bazai yiwuba wace hanya zanbi in nemo NIN number ta?
Wslm.
DeleteKaje office din National Identity Card Management mafi kusa don gabatar da korafinka.
Assalam dan Allah Mutun yana iyayin Register katin ɗan ƙasa a intaner?
ReplyDeleteNational id card
DeleteOK Dan allah yazanyi na sauke wannan app din , nayi kokarin saukeshi a play store amman yakiyi sai sachin yakeyi kawai
ReplyDeleteMungode
ReplyDelete