HANYOYIN DAZAKA SAMU KUDI A YOUTUBE
Assalamu Alaikum.🙏🙏🙏🙏🙏
❤Barkanmu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka.
💥Sakamakon yawan tambayoyi da mabiyan mu masu albarka suke turomana dangane da yadda ake samun kudi a Youtube, yau InshaAllahu zamuyi takaitaccen bayani akan Youtube.
💥ME NENE YOUTUBE.
Youtube wata kaface ta sadarwa a yanargizo wadda ta shahara wajen watsa manufofi da suka shafi rayuwar yau da kullum, ana amfani da Youtube wajen yada videos da makamantansu don tallata hajja ko yada manufa, ana amfani da Youtube akan dukkan abubuwan da suka shafi rayuwarmu ta yau da kullum. Shahararrun mutane na yin amfani da Youtube don isarda sakonni Kaitsaye ga masoyansu.
Hakazalika anyi itifakin cewa youtube yana dauke da rabin yawan mutanen da suke hawa internet, bincike ya nuna cewa a duk watan duniya mutum 1.9 billion ne suke hawa youtube, sannan kuma ana dora bidiyo mai yawan awa 500 a kowane minti.
🔥YADDA ZAKAI RIGISTA A YOUTUBE
Zaka iya yin register a Youtube don yada manufofinka ko tallata hajjar ka, don yin register shiga nan .
👉Akwai sharudan mallakar youtube account sune kamar haka.
👉Matakin farko saika haura shekaru 18 a duniya.
👉sannan kuma Sai kana da Email adress.
👉Sannan sai ka kiriri Account/ Channel dinka a youtube a nan .
👇IDAN KANA SON SAMUN KUDI A YOUTUBE SAI KA CIKA WADANNAN SHARUDDAN.
🎈Bayan ka mallaki account ko Channel dinka a youtube zaka samu damar amfana da tsare-tsaren youtube masu faida sosai.
👉Katabbata Account/Channel dinka ya cika dukkan sharuda misali dole sai mutun Akalla 1,000 sun yi suscribing din Channel dinka sannan kuma mutun 4,000 sun kalli abunda kadora tsawon shekara daya.
📍Sannan saika saita abunda ake kira Adsense shine mafi sauki wanda zaka samu damar samun kudi duk lokacin da mutane masu yawa suka kalli hajjarka. Don yin register Adsense shiga nan.
📍Ko kuma kazama youtube partner Don zama youtube partner shiga nan.
📍Bayan Kacika dukkan shariddan Adsense. Dole saika dora abubuwa (videos) masu daukar hankali, wanda mabiyanka zasu dinga kalla akaiakai, kuma hakan zai jawo hankali sababbin subscribers.
🎈Super Chat payments: idan kanason mabiyanka (subscribers) su dinga comment kaitsaye lokacinda kake watsa shirye-shiryenka sannan kuma za a dinga biyanka wani abu, sai ka shiga tsari super chat payment.
🎈Bayan kacika wadancan sharudan Adsense zasu baka damar samun kudaden waddanda zasu dinga biya kai tsaye a account dinka.
🎈Hakazalika zaka iya tallata hajar ka a youtube don samun kostoma.
🎈Ko kuma Kakirkiri wani abu da za adinga kalla akai-akai.
📍Zakuma ka iya dora video ko wani makamancin haka wanda suscribers naka zasu biya kafin su kalla. Don shiga tsarin shiga nan.
📍Zakuma ka iya yiwa hajarka register a youtube don tallatawa. Don Samun dama shiga nan.
📍Akwai hanyoyi da yawa da zaka samu kudi a youtube.
Wassalam.🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
Don samun shirye-shiryen kai tsaye a email dinku zaku iya subscribe na site din mu a sama, ko ku tura da sakon email zuwa 👇Duniyarwaya7@gmail.com
Ko 👇
Ko👇
Ko👇
Comments
Post a Comment
Thank you for your comment