YADDA ZAKA TSARE LAYIN WAYARKA (SIM LOCK).

Assalamu Alaikum.

Barkan mu dasake saduwa a wannan shafi mai albarka.πŸ™πŸ™πŸ™πŸ™πŸ™

InshaAllahu yau zamuyi cikakken bayani akan yadda zaka tsare lain wayarka,  wato (SIM LOCK).

A wannan zamani da muka samu kanmu acikinsa wayar hannu πŸ“΅ taza ma aba mai mahimmanci, musamman agurin waddanda suke da asusun ajiya a bankuna,  yanzu kusan mafi yawanci hada-hadar kudade a kan wayaπŸ“΅ a ke gudanarda su,  wannan daliline yasa wasu mutane masu mataciyar zuciya😑 kullum suke kara kir-kiro hanyoyin da zasu cuci mutane.

Abune mai sauki a gurin irin waddannan mutane  su fisge wa mutum wayaπŸ“΅, kokuma su kwata ta karfi,  ko kuma su sace ta, wasu suna satar waya πŸ“΅don su siyar su samu kudi wasu kuma suna sata ne don suyi amfani da layin wayarka wajen sace maka kudade a cikin asusun ajiyarka na banki.⭕

Irin waddanda suke sacewa don su sacewa mutun kudade suna daukar lokaci mai tsawo wajen samun wasu bayanai agurin mutum,  kamar Account number,  BVN, ko shekarun haihuwa da sauransu,  bayan sun gama samu irin waddannan bayanai sai su sace maka waya,  ko su kwata ta karfi,  ko kuma su fisgeta a hannun ka πŸ“΅.
Yana da kyau ka tsare layin wayarka musamman idan kana ajiye yan kudadenka a banki,  tayadda koda an sace maka waya baza a iya yimaka sata a asusun ajiyarka ba,  koda kuwa wanda ya sata din yasan Account numabarka da sauran bayanan ka. 🚷

YADDA ZAKA TSARE LAYINKA.
dafarko dai kashiga setting a wayarka sai ka shiga security setting,  πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
saika shiga sim lockπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
saikai locking din sim dinkaπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
idan kai locking din SIM dinka zasu bukaci ka saka pin dinka saika saka 00000 shine default pin dinka,  idan baiyiba   saika nemo SIM certificate dinka saika saka PUK dinkaπŸ“πŸ‘‡πŸ‘‡
bayan ka saka PUK din zasu tambayeka ka zabi pin guda 4 sai ka saka idan ka saka pin guda 4 sazu ce ka maimaita idan ka maimaita shikenan ka rufe layinka.

FAIDOJIN KULE  LAYI
Bayan  ka saka pin guda hudu to duk lokacin da ka kashe wayarka ka kuna sai ka saka wannan pin din guda 4, .
Koda an sace maka waya da niyar ayi amfani da layinka ba za a samu damar yin amfani da layinba,  saboda wanda ya saci wayar bai san pin dinka ba kuma dole sai an saka pin din layin zai yi aiki.

Idan baka san inda SIM certificate dinka yakeba kuma ka manta PUK dinka sai ka kira customer care na kamfaninka.

Missali
 MTN :180

Airtrl :111/121

9 mobile  :200

Glo :121/200

Wassalam.
Don bibiyar shirye-shiryen mu zaku iya suscribing site din mu, ko ku tura sako zuwa :duniyarwaya7@gmail.com
Ko 
ko 
Telegram 

ko 


Comments

Popular posts from this blog

YADDA ZAKA SAI KATI KO TURA KUDI DAGA BANK ACCOUNT DINKA

YADDA ZAKAYI TARaNSFAR DATA DAGA LAYINKA ZUWA WANI LAYI

YADDA ZAKA DAWO DA FACEBOOK ACCOUNT DINKA DA AKA KWACE