Posts

Kashi na daya

NITDA ACADEMY ZASU BAWA MATASA MILLION UKU ILIMIN NAURAR ZAMANI DA FASSAHAR ZAMANI KYAUTA

Image
Assalamu alkaimu. Barkan mu da sake saduwa a wannan dandali . Hukumar Dake Bada horo akan Ilimin Fasahar zamani ta Nigeria wato NITDA zasu bawa matasa miliyan uku horon akan Ilimin Fasahar zamani, daga Yan shekara 18-50 . Ayanzu haka an Bude shafin yin register don fara Bada wannan horon. Abubuwan da ake bukata . 1. Kasance Dan shekara 18-50 2. Email 3. Lambar waya. 4. NIN/BVN 5.Computer/ Android Za a Bada horon akan waddannan fannoni kamar yadda suke a wannan hoton Na kasa 👇 Bayan kamla karatu zaa bada certificate. Don yin register shiga nan Don Allah Yan uwa a daure ayi register. Allah yasa mudace 

YADDA ZAKAYI RIGISTAR KATIN ZABE ONLINE

Image
Assalamu Alaikum. Barkanmu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, Yau insha-Allahu zamuyi bayani akan yadda zakayi register katin zabe online,  Hukumar zabe ta Kasa taba sanarwar bude sabon shafi a yanargizo wanda yan Nigeria zasu yi registar, anbude shafinne sakamakon cutar covid-19 don rage cinkoso a guraren rigistar. Hakazalika koda kadade dayin register zaka iya canja wasu bayanai akan katin zaben ka ko kacanja mazaba, missali idan kayi regista a wata jaha yanzu kuma kanason ka koma wata jaha zaka iya canjawa  da kanka akan yanar gizo. ✳️ Don yin register sabon katin zabe shiga nan   ✳️ Idan kadade da yin registrar aman bakasan matsayin katin zaben kaba shiga nan don duba matsayin katin ka . ✳️ Idan da kayi regista a wata jaha yanzu kuma kana son chanja jaha da mazaba shiga nan   ✳️ Idan da kayi regista kuma ka karbi katinka aman ya bata to kagarzaya office din INEC mafi kusa zasu baka form kacika Kuma zasu baka wani.  ✳️ idan kana da wani...

MATAKIN DA YADACE KA DAUKA IDAN AN SACE MAKA WAYA KO KUMAKAGA ANA CIRE MAKA KUDADE A ASUSUN AJIYARKA NA BANKI.

Image
Assalamu alaikum. Barkanmu dasake saduwa a wannan shafi mai albarka,  yau InshaAllah zamuyi takai taccen bayani akan matakan da ya kamata ka dauka don tsare kanka daga sharin masu sacewa jamaa kudade a asusun ajiyar su na banki. Kasancewar yanzu kwacen wayar hannu yazama ruwandare a kullum sai kaji wani yace an tare shi  an kwace masa waya ko kuma an sace,  wanda kuma daga baya sai wanda ya saci wayar yayi amfani da layin kan wayar ya sace wa mai wayar kudaden sa acikin bankinsa na ajiya. Yanada kyau kafin a sace maka waya ka tabbata ka sakawa layin wayarka lambobin tsaron tayadda koda ansace wayar baza a iya amfani da layinba wajen yi maka sata a asusun ajiyarka. Bincike ya nuna mafiyawan kwacen wayoyin hannu da akeyi yanzu anayi ne don a samu damar yin amfani da layin kan wayar don sacewa mai wayar kudadensa a asusun ajiyarsa na Banki. Wannan matsalar tafaru da dubban mutane wadanda bayan an sace musu waya anyi amfani da layin su wajen sace musu kudade a asusun ajiyar s...

KARATUN DEGREE KYAUTA

Image
Assalamu Alaikum ,  Barkanmu dasake saduwa a wannan shafi mai albarka,  yau insha Allah zamu sake yin bayani akan wani  Schoolarship wanda Kasar Egypt Take bawa kasahen Africa hadda Nigeria.  Nigerian supreme council  for islamic affairs ta wallafa a shafinta na facebook.  Don samun karin bayani ziyarci shafin  https://www.facebook.com/518483651546171/posts/3853184504742719/ Don yin Register shiga nan.  https://docs.google.com/forms/u/0/d/e/1FAIpQLSce35bPA3nWJQkitLJXMDeaIi4e1Sr41vp_oG_V5SkNLe1RTg/viewform?usp=send_form Don Allah Yan Uwa a watsa ko Wasu sa amfana. Mungode. Don bibiyar shirye-shirye mu zaku iya shiga Telegram group t.me/duniya100

YADDA ZAKAI KARATUN DIGIRI /MASTERS KO PhD KYAUTA

Image
Assalamu Alaikum. Barkanmu da sake saduwa a wannan shafi  mai albarka,  yau InshaAllah zamuyi  bayani akan yadda zaka samu damar yin karatun degree ko masters hadda  Phd kyauta a duk inda kakeso a fadin duniya wanda Islamic Development Bank suke daukar nauyi duk shekara. Islamic  Development Bank wata ma'ajiyace ta kudi wada take da shalkwata a Saudi Arabi kuma tana karkashi Organisation of islamic Counyries (OIS) wanda  ya kunshi kasashe 57 aduniya hadda Nigeria. Islamic Development Bank ankafatane  shekarar 1973 wanda suka dade suna dåukar nauyin karatun yayan masulmi a fadin duniya.  Islamic Development Bank sunbude portal dinsu don bawa dalibai damar cika form din scholarship don daukar nauyin karatunsu a shekara 2021 kuma ayanzu haka saura kwana 50 a rufe portal din.  Gamasu sha'awar karo karatu kuma basu samu damaba  sakamakon wasu dalilai to ga dama ta samu don cigabada da karatu. Gamasu shaawa  zasu iya ziyartar ...

YADDA ZAKA SAKA LAMBAR KATIN DANKASARKA AKAN LAYINKA NA MTN

Image
Assalamu Amaikum,  Yau insha Allah zamuyi bayani akan yadda zaka saka Lambar National Identity Card dinka a kan layinka na MTN. sakamakon umarnin da Maigirma Ministan Sadawar Dr. Aliyu Isah Fantami yabayar na rufe dukkanin layin  da baa saka lambar shedar katin dankasaba akansa ba,  Daga yau zuwa karshen watan December, 2020. kamfanin MTN sun fitar da sabon link din da zaa ziyarta don saka lambar katin dan kasarka. Idan kana da katin dan kasa kuma baka saka lambar katinkava,  ka shiga wannan link din https://mtnonline.com/nim/  zakaga wani form sai ka cika kayi submitting.  Ko kuma ka danna * 785 # akan wayarka sai ka saka lambobin katin dan kassarka.  Idan kuma ka manta lambar katin dan kasarka ka danna * 346#  akan layin da kai registar katin dan kasarka zaka ga lambar. Wassalam. Don samun shirye-shieyen mu kaitsaye a email dinku zaku iya suscribing din shafin mu a sama. Ko ku biyo mu a Telegram t.me/duniya100 Youtube...

KARATU A SAUKAKE

Image
Assalamu alaikum. Yau InshaAllah zamuyi bayani akan yadda zakayi karatu kyauta online. Al-Madrasatu An-Nabawiyyah RC 2763063 Makarantace dake koyar da ilimin addinin musulunci da kuma ilimin koyan harshen larabci. Hukumar makarantar ta bude online class inda dalibai zasu ringa daukar darasi online, kana gidanka zaka koyi karatu cikin sauki, wani bawan Allah maisuna  Abu Mardiy Kewdirôrun At-thaqoofiy shi ya dauki nauyin karatun, duk dalibin dayai registar basai yabiya kudiba,  aman idan kana bukatar yin dukan kwasakwasan zaka biya kudin da basu wuce naira 4200 akan kowane kwas,  kuma idan ka kammala za abaka certificate, sannan kuma idan kana bukatar zuwa kasar saudi Arabia don karo karatu, zaka iya amfani da wannan certificate din da aka baka kuma zasu baka admission da wannan certificate a kasa mai tsarki. hakazalika tsarin koyarwar ma iri dayane da na Jamion Kasar saudi Arabia. YADDA AKE DAUKAR DARUSSA   👉  akwai Audio  👉akwai  Pdf...

KARIN BAYANI AKAN C.A.C REGISTRATION

Image
Assalamu Alaikum. Dangane da bayanin da mukayi abaya akan C.A.C wato shedar yiwa kamfani ko masana'anta register, a yanzu abun yazo da sauki ba sai kaje office dinsu ba. Wannan form din kawai zakai dowload. bayan  kayi dawnload saika cika da biro sai kayi scaning din form din saika tura zuwa ga email din hukumar C.A.C akwai email address na jahohi 36 a hoton kasa . Ga na Kano coachmusty96@gmail.com sai ka zabi na jaharka sai ka turo, bayan wani lokaci zasu turamaka da sako ta email ko layin wayar ka. Don Allah yan uwa a daure a yi registar.  TALLAFIN KUDI GA MASU SANA OI Join us on t.me/duniya100 Youtube  https://m.youtube.com/channel/UCuoL5N36WaYqiaiIDxXdErg

TALLAFIN KUDI GA MASU SANA'OI

Image
Assalamu alaikum . Yau insha Allah zamuyi bayani akan talafin zunzurutun kudi har  billion sabain da biyar 75billion naira d a Gwamnatin tarayya ta kudiri aniyar bawa matasa afadin kasar nan. Wannan tallafin an bashi suna " Nigerian youth investment fund "an kuma kaddamar dashine don amfanin matasan yan shekara  18  zuwa  35  waddanda suke da masana antu mallakar kansu. Tunidai an bude shafin da akeyin registar. Ga masu bukata zaku iya ziyartar shafin don yin registar .👇 https://t.co/CSyDmULTKr?amp=1 Yan uwa a daure ayi regida. TALLAFIN KARATU KYAUTA Don samun darrussanmu zaku iya bibiyarmu a  Telegram t.me/duniya100 Facebook  

TALLAFIN KARATU KYAUTA

Image
Assalamu Alaikum . Yau insha Allah zamuyi bayani akan yadda zaka samu damar yin karatu a kasar waje kyauta. A kokarin da Gwamnatin tarayya takeyi na ganin ta inganta harka ilimi a Nigeria,  Gwamnatin tarayya tabawa ministan ilimi umarnin tallafawa matasa masu sha'awar yin karatu a kasashen waje,  wato a karkashin tsarin  scholarship . Kowanne dankasa nada dama ya nemi wannan tallafi wanda yahada daliban dasuka kammala karatun sikandire kuma suka samu sakamako mai kyau tare da samun  credit 5 . Haka zalika wadanda suka gama degree, ma zasu iya neman wannan tallafi don karo karatu a kasashen waje. Ga masu bukata zaku iya ziyartar shafin ma aikatar ilimi ta kasa don yin regista 👇 https://fsbn.com.ng/scholarships Wassalam. Zaku iya suscribing din shafin mu  Telegram. t.me/duniya100 Facebook https://www.facebook.com/groups/197116404183415/?ref=share Bayani akan yadda aka tsare layin wayarka

YADDA ZAKA SAMU C.A.C KYAUTA

Image
Assalamu Alaikum. Barkanmu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka. Yau inshaAllah zamuyi bayani akan yadda zaka samu certificate na Coperate affairs C.A.C . Kyauta Akokarin da Gwamnatin Tarayya takeyi na tallafawa masu Manya da kananan masana'antu a fadin kasar nan don ganin sun dogara da kansu,  Gwamnatin Taraya ta bawa hukumar cooperate affaires commission umarnin yiwa masu Manya da kananan masa na'antu (250,000) registar C.A.C kyauta a fadin kasar nan.  YADDA ZAKA SAMU REGISTA Idan kanada masana'anta kuma baka da C.A.C certificate (wato shedar mallakar masana'anta) sai ka garzayya ofishin Cooperate Affairs Commission , don yin Regista kyauta don samun damar amfana da tallafin da Gwamnatin Tarayya take bawa masu kananan masana'antu. Don Allah jama'a a daure a mallaki wannan certificate din don amfanin kanmu. Mungode. Wassalam. Zaku iya suscribing din shafin mu. A Telegtam t.me/duniya100 ko Facebook 

KANA BUKATAR KOYAN ILIMIN COMPUTER DA YANAR GIZO

Image
Assalamu Alaikum YAN NAJERIYA GA DAMA DAGA PANTAMI  Maigirma Ministan Sadarwa da Tattalin arziki ya kaddamar da manhajar yanar gizo da ta wayar hannu, ga yan  Najeriya domin samun garabasa wajen koyan sana'o'i iri-iri na zamani, da samun guraren aiyukan yi cikin sauki, kuma an tsarashi yadda zaka koya da kanka tahanyar bidiyo da rubutu, wannan tsarin yanada matukar mahimmanci da kuma amfani sosai ga al'ummar Najeriya. Wannan tsari yanada saukin fahimta da kuma saukin amfani ga mai aiki da shi, sannan ba sai kana da data a wayar ka ko Computer kaba zaka iya shiga tsarin, tsarin ankasa shi kashi uku ne akwai  #Digital_Nigeria akwai  #NITDA_Academy da kuma #IBM_Digital_for_Africa, ko wanne yana da mahimmanci kuma za'abaka certificate bayan kammala training din. Ga yadda tsarin ko wanne yake da yadda za'ayi amfani da manhajan da kuma amfaninsu ga yan Najeriya.   #DIGITAL_NIGERIA Shi wannan tsarin yana da tsarurruka da yawa a kasa dashi, zaka koyi sa...

KARIN BAYANI AKAN TALLAFIN SURVIVAL FUND.

Image
Assalamu alaikum Barkan mu dasake saduwa a wannan shafi mai albarka. 🙏 Kamar yadda mukayi alkawari zamuyi bayani akan hanyoyin da za'a bi wajen mallakar CAC , TIN ,  da SMEDAN N0. waddanda ake bukata don yiwa masana anta Register don amfana da tallafin da zaa bawa masu kanan masa na antu a fadin kasar nan. Kamar yadda gwamnatin taraya tayi alkawari. Wanda ake kira da survival funds. ABUBUWAN DA AKE BUKATA 1. cooperate affairs commission  (CAC) . idan baka da CAC sai ka garzaya office din cooperate affairs don yin Register, don karin bayani shiga nan 👇 https://services.cac.gov.ng/login 2.Small and mediu enterprises development Agency of Nigeria ( SMEDAN N0. ), smedan ba sai kaje office dinsuba zaka iya yin Register online aman dole sai kana da email,  namabar waya,  da sunan masana anta. Don yin Register shiga nan 👇 https://smedanregister.ng/register 3.Taxt Identification Number (TIN N0). Zaka iya zuwa office din su ko kuma ka gwada online idan kayi s...

TALLAFI GA MASU KANANAN MASANA'ANTU

Image
Gwammnatin tarayya ta kudiri aniyar bada tallafi ga masu kananan sanao'i a fadin kasarnan. ABUBUWAN DA AKE BUKATA  1. Dole sai kanada massana'anta. 2. Dole sai masana'antarka tana da suna. 3. Dole sai kayi Register da cooperate affairs Kuma sai anbaka shedar (C.A.C). 4. Dole sai kana da Taxt Identification N0. (TIN). 5. Dole sai kayi Register da hukumar small and meduim interprises development agency (SEMDAN). kuma sai ka mallaki SMEDAN N0. 7. Dole sai kanada cooperate account da sunan masana'antarka 8. Dole sai kana da BVN. 9. Dole sai kanada email address 10. Dole sai kana da akalla mutum 5 suna aiki a karkashinka. 11. Dole sai kanada layin waya. Waddannan sune mafi yawancin abubuwan da ake bukata. Donyin Register  shiga nan https://www.survivalfundapplication.com Karin bayani akan survival fund 👇 https://auwalaliyu.blogspot.com/2020/09/assalamu-alaikum-barkan-mu-dasake.html?m=1 Kadan daga cikin darussan mu 👇 1. Yadda zaka duba katin dan kasarka 👇👇👇👇...

YADDA ZAKA TSARE LAYIN WAYARKA (SIM LOCK).

Image
Assalamu Alaikum. Barkan mu dasake saduwa a wannan shafi mai albarka.🙏🙏🙏🙏🙏 InshaAllahu yau zamuyi cikakken bayani akan yadda zaka tsare lain wayarka,  wato (SIM LOCK) . A wannan zamani da muka samu kanmu acikinsa wayar hannu 📵 taza ma aba mai mahimmanci, musamman agurin waddanda suke da asusun ajiya a bankuna,  yanzu kusan mafi yawanci hada-hadar kudade a kan waya📵 a ke gudanarda su,  wannan daliline yasa wasu mutane masu mataciyar zuciya😡 kullum suke kara kir-kiro hanyoyin da zasu cuci mutane. Abune mai sauki a gurin irin waddannan mutane  su fisge wa mutum waya📵, kokuma su kwata ta karfi,  ko kuma su sace ta, wasu suna satar waya 📵don su siyar su samu kudi wasu kuma suna sata ne don suyi amfani da layin wayarka wajen sace maka kudade a cikin asusun ajiyarka na banki.⭕ Irin waddanda suke sacewa don su sacewa mutun kudade suna daukar lokaci mai tsawo wajen samun wasu bayanai agurin mutum,  kamar Account number,   BVN, ko shekarun haihuwa ...

DAMA GA MASHU SHA'AWAR SHIGA AIKIN SOJAN KASA

Image
Ranar  litinin mezuwa wato 14/9/2020 za'a bude  daukar aikin sojan kasa. Hukumar Sojojin Nigeria ce ta wàllafa sanarwa a shafinta na facebok.   https://www.facebook.com/354312648014400/posts/2995420023903636/ Gamasu shaawar shiga aiki soja zasu iya ziyartar wannan website don yin registar  .

HANYOYIN DAZAKA SAMU KUDI A YOUTUBE

Image
Assalamu Alaikum .🙏🙏🙏🙏🙏 ❤Barkanmu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka. 💥Sakamakon yawan tambayoyi da mabiyan mu masu albarka suke turomana dangane da yadda ake samun kudi a Youtube, yau InshaAllahu zamuyi takaitaccen bayani akan Youtube. 💥ME NENE YOUTUBE . Youtube wata kaface ta sadarwa a yanargizo wadda ta shahara wajen watsa manufofi da suka shafi rayuwar yau da kullum, ana amfani da Youtube wajen yada videos da makamantansu don tallata hajja ko yada manufa,  ana amfani da Youtube akan dukkan abubuwan da suka shafi rayuwarmu ta yau da kullum. Shahararrun mutane na yin amfani da Youtube don isarda sakonni Kaitsaye ga masoyansu.  Hakazalika anyi itifakin cewa youtube yana dauke da rabin yawan mutanen da suke hawa internet, bincike ya nuna cewa  a duk watan duniya mutum 1.9 billion ne suke hawa youtube, sannan kuma ana dora bidiyo mai yawan awa 500 a kowane minti. 🔥YADDA ZAKAI RIGISTA A YOUTUBE Zaka iya yin register a Youtube don yada manufofinka...

KANA BUKATAR TALLAFIN NOMA

Image
Assalamu Alaikum. Barkanmu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, yau InshaAllah zamuyi bayani akan wani tallafin noma wanda babu interest wanda akabawa suna 'Manaraabp' wanda yake karkashin kungiykyin addini kuma kowa zai iya cikawa.  Website na Manaraabp gaskiyane, kuma ya  umurci kamfanin Manara da  jagoranci wannan tsari na karbar bashi mara kudin ruwa da  malamai suka yi ta kai ruwa rana akan samuwar sa, domin musulman kasar nan su amfana da bashin. kuma babban bankin kasa CBN  ya amince zai bada talafin da babu interest ga masu sha'awa.  Dan haka kowanne dan kasa mussaman musulmi zai iya ziyartar  wannan  Website   din don yin register  duk Wanda ya ga wannan sakon ya daure ya cika, kuma ya sanar da 'yan uwa su cika. Nan gaba kadan za'a kira taron tantancewa a jihar da mutun yake.  Kamfanin Manara shi ya dauki nauyin wayar da kan mutane, tare da jagorantarsu. Ba'a karban ko kwabo wajen cikawa, kuma babu tsarin ...

KANA BUKATAR SAMUN TALLAFIN KARATU KYAUTA A KASAR SAUDIYA.

Image
Assalamu alaikum. Barkan mu dasake saduwa a wannan shafi mai albarka. Kasancewar matasa da yawa suna son yin karatu aman basu samu dama ba saboda wasu dalilai waddanda suka hada da rashin gata da makamantansu, saboda hakane kamar yadda ta saba kasar saudi Arabia ta kudiri aniyyar talafawa matasa mussaman a kassahem musulmai don daukar nauyin karatun su akan dgree kyauta,  wanda hakan zai bawa marasa gata damar samun ilimin degree akan kwasakwasai da dama. A halin yanzu dai sun bude portal din da zaku iya ziyarta don yin rigista don samun damar karo karatu kyauta.  Dan samun cikakken bayani akan yadda zaku yi regista ku shiga nan . Mungode dafatan Allah ya bada saa. Don samun shirye-shiryen mu kai tsaye a email din ka kai suscribe din fegin mu. Ko  Facebook ko  Whatsapp  Ko  Telegram   Wassalam. 

YADDA ZAKA DUBA LAMBAR KATIN SHEDAR DAN KASAR KA AKAN WAYARKA.

Image
Asalamu Alaikum. Barkanmu dasake saduwa a wannan shafi mai albarka. Yau InshaAllahu zamuyi bayani akan National Identity Card wato katin shedar  dan kasa. Kasancewar yanzu kusan duk wani abu dazakayi amatsayinka na dan kasa sai anbukaci shedar katin dan kasa,   Kusan yanzu babu wani abu dazakayi sai an bukaci shedar katin dan kasa,  ta kai matakin da ko aiki zaka nema sai ka yi amfani da shedar katin dan kasa,  idan zaka bude account a banki ,  ko zakayi welcome back na layinka da yabata sai ka nuna shedar katin dan kasa.(da sauransu). Kullum abubuwa cejawa sukeyi,  nan gaba kadan ma idan baka da shedar katin dan kasa akwai yiwuwar a ki baka admission a makaranta,  ko kuma a hanaka zirga-zirga a fadin kasar nan, don haka yanada kyau kowa yadaure yayi. YADDA ZAKA DUBA LAMBAR NATIONAL ID DINKA AKAN WAYARKA. mafiyawan lokaci mutane  da dama  suna manta lambar katin dan kasar su sakamakon wasu dalilai wani lokacin ma zakaje kayi...

YADDA ZAKA SAN ABUNDA YAYANKA SUKEYI AKAN WAYARSU TA WAYARKA

Image
Assalamu Alaikum. Barkanmu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka,  dafatan muna cikin koshin lafia,  Amin. Bayan haka yau InshaAllahu zamuyi bayani akan wani tsari da kamfanin  google suka kirkiro wanda ake kira da " google family link "  wannan tsari google sun kirkiro shi do karfafa alaka a dangi ta yadda kowane member na family zai dinga samu bayanai akan yan uwansa wanda ya hada da location, activities, da kuma events. A wannan tsari google sun ware wani bangare da sukakira da " parental control" wato yadda iyaye zasu dinga kulawa da irin abubuwanda yayansu suke akan wayar su wato smart phones. Awannan tsari na parental control iyaye  za su iya hana yayansa saka  wasu app da basu yadda da suba,  kuma za su iya hana yayansa ziyartar wasu shafikan da basu amince dasuba,  haka zalika iyaye zasu iya sanin dukkan abubuwanda yayansu suke gudanarwa akan wayarsu. Parental control zai taimaka sosai wajen hana kananan yara ziyartar shafikan da basu...

DAMA TASAMU GA DALIBAN KIMIYYA DAFASAHA

Image
Assalamu alaikum. Barkanmu dasake saduwa a wannan shafi mai albarka. Yau InshaAllahu zamuyi bayani akan scholarship wanda hukumar makarantar Jamiatul Almadinah dake kasa mai tsarki ta wallafa a shafinta na yanar gizo, inda tabada sanarwar bada tallafin karatu kyauta ga dukkanin dalibin kimiyya da fasaha ga wanda keda sha 'awar zuwa kasar don samun kwalin digiri. Hukumar tace zata dauki nauyindalibai daga dukkan fadin duniya don samun digiri akan ilimin kimiyya da fasaha. Hakazalika hukumar tace zata dauki nauyin daliban da suka cancanta, wanda yahada da karatu kyauta,  gurin kwana kyauta, sannan kuma zasu bawa kowanne dalibi kudin kashewa har tsawon shekaru biyar.  YADDA ZAKAYI APPLYING akwai sharuda da dama akan tsarin application din zaka iya ziyartar shafinsu a nan  don samun cikakken bayani. Dafatan Allah bada saa,  yan uwa adaure ayi applying. Wassalam . Don samun shirye-shiryen mu  a email din ka kayi subscribe din shafin mu. Ko ka ...

ZA ABUDE DAUKAR AKIN POLICE A WANNAN SATIN

Image
Ajiyane rundinar yansanda ta kasa wato "Nigeria Police" ta sanar da aniyarta na daukan sabin ma aikata a hukumar,  hukumar ta bada sanarwar ne a shafinta na facebook a jiya inda ta wallafa cewar za'a bude website din ranar 14/07/2020.  Ga yadda tsarin daukar aikin zai kasance a wannan hoton na kasa. dafatan Allah yabada saa amin. Mungode. 

KOKASAN AMFANIN DO NOT DISTURB AKAN WAYARKA TA ANDROID

Image
Assalamu alaikum. Barkanmu da sake saduwa a wannan dandali dafatan muna cikinkoshin lafiya. Yau inshaAllahu zamuyi bayani akan wani abu akan wayar android wanda akafi sani da  "do not disturb"  Do not disturb nada amfani sosai akan wayar android wanda yahada da rage yawan kiran da zai shigo wayarka, rage tsawon ring tons din wayarka,  ko alarm, ko sakonin dasauransu. Missali idan bakason wani ko wasu su kiraka awaya kawai sai ka zabi adadin contacts da kake son amsa kiransu a wani lokaci, saiaka sakasu wadanda bakason amsa kiransu a dont disturb kuma idan za ka shiga masallaci ko meeting aman bakason wani ya kira ka ko kuma kanason ka rage tsayin ring ton dinka tayadda kawai zaiyi   yi kara kadan kawai saika saka wayarka a donot disturb saika satai yadda kakeson ya kasance. Akwai tsare tsare kamar haka  zaka iya saita lokacin da bakason wayarka tai ringi ko kuma baka son wasu daga cikin contacts dinka su kiraka. Kamar haka. ...

YADDA ZAKA SAMU 20 GIG AKAN KUDI 3500

Image
Assalamu alaikum  Barkanmu dasake saduwa a wannan dandali.🙏🔦 Yau zamu bayani akan yadda za ku sami data 20gig akan kudi Naira 3500.👇 MTN sun fito dawani tsari da suke kira my offer wanda yabawa kwastoma damar samun 20gig a akan kudin Naira  3500👇 Ita dai wannan data tana kaiwa har tsawon wata 1👇 Haka zalika zaka iya samun 2gig akan kudi Naira 500 wada zakayi amfani da ita tsawon sati 1 kacal.👇 Wannan tsari yafi dacewa ga masu Downloading file mai nauyi,  ko finafinai 👇 Masu yawan kira a waya zasu iya amfani da wannan tsari don samun linki 5 na katin da sukasaka. 🙋 Missali idan kasaka 1000 zasu baka 5000.👇 Gargadi 🚯 Wannan tsari ba a kowane layi yakeyiba aman yanayi a mafiyawan layikan MTN.😀 YADDA ZAKA SHIGA TSARIN danna * 121 # akan wayar ka zaka ga sununamaka kamar haka 👇 Idan na kira kake so zaka ga sun nunamaka kamar haka 👇 Wassalam  Fatan alkairi ga masu bibiyar shafin mu🙏 Mungode 🙌 Zaku iya bibiyar shirye shiryen mu...

YADDA ZAKA SAMU DATA KO BONUS NA KIRA AKAN FARASHI MAI SAUKI A LAYIN MTN

Image
Assalamu alaikum, barkanmu dasake saduwa a wannan shafi yau InshaAllah zamuyu bayani akan yadda zaka samu data mai sauki a layinka, Ko samun bonus mai yawa akan farashi mai sauki . zamufara da MTN . A kokarin su naganin sun saukakawa kwastomomin su MTN sun fito dawani tsari wanda suke kira "my offer", a wannan tsarin zaka samu data mai sauki ko kuma bonus na kira mai yawa akan farashi mai sauki,  Zaka iya samun 1.5 gig a kan kudu nera 300 wada zaka iya amfani da ita tsawon sati 2. Zakuma ka iya samun 6gig akan 2000 tsawon wata 1 Ko kuma 10gig akan 3500 Hakazalika zaka iya samu bonus na kira mai yawa wato idan kasaka dari 200 zasu baka 1000 idan kasaka 400 zasu baka 2000 , da sauransu Yadda zaka shiga wannan tsarin ka danna * 121# zakaga su nuna maka zabi kamar haka. Saika zabi wanda kake so  idan kazabi 2 wato tsarin data zasu sake baka zabi kamar haka  saika zabi wanda kakeso Kawai zasu baka datar daka ke so . Idan kuma bonus din kira ne...

BAYANI AKAN LAMBOBIN SIRI NA WAYAR ANDROID

Image
Assalamu alaikum, Yau InshaAllah zamuyi bayani akan wasu lambobi siri na wayar android wanda idan ka danna zaka samu bayanai masu faida dangane da wayarka ta android, Waddannan  lambobi sune kamar haka:- ✅*#*#4636#*#* bayani akan batirin waya. ✅*#*#7780#*#* goge dukan abubbuwan dake kanwa ✅*2767*3855#  goge komai na kan waya tare da maida ita kamar yadda take a farko. ✅*#*#34971539#*#* bayani akan kyamara ✅*#*#7594#*#* Changing the power button behavior-chanza tsarin kunawa da kashe waya ✅*#*#273283*255*663282*#*#* don saurin samun kofin abubuwan dake kan waya akan memori kad ✅*#*#197328640#*#* gwada karfin netwok ✅*#*#232339#*#* OR *#*#526#*#* Gwada waifi ✅*#*#232338#*#* nuna adreshin waifi ✅*#*#1472365#*#* nuna saitin guri ko gari ✅*#*#1575#*#* satin wani guri ko gari ✅*#*#0283#*#* dawo da farkawar wata daidai ✅*#*#0*#*#* saita kalolin waya ✅*#*#0673#*#* OR *#*#0289#*#* Saita sauti ✅*#*#0842#*#* saita babureshin da fitilar baya ✅*#*#266...

YADDA ZAKA MAGANCE MATSALAR BATTAN TAKADDUN KA

Image
Assalamu Alaikum. Barkanmu dasake saduwa a wannan dandali,  yau InshaAllah zamuyi bayani akan hanyoyin dazakabi don magance matsalar batan takaddun makarantar ka ko kuma wasu takaddu masu mahimmamci a rayuwar mu tayau da kullum. Kasancewar dan adam yanada mantuwa, wanilokaci sai ka ajiye abu kuma ka manta a inda ka ajiye,  ta iyayiwuwa kuma lokacin da bugatar abun zata taso sai ka manta a ina ka ajiye,  wani lokaci kuma,  ana iya samun matsala ta batan takaddun kokuma ibtilain gobara ko wani abu makamancin hakan. Wasu lokutan kuma zaka iya yin tafiya don neman aiki ko wani abu makamancin hakan aman sai ka manta da wata takadda da bata taka kara ta karya ba kuma watakila dole se da ita za kasamu abun da kakeso. Yana da kyau ka bi wadannan hanyo don magance irin wannan mtsala. 1. Ka yi scanning din dukkan takaddunka ka ajiye su a cloud storage (wato ma'ajiya ta yanar gizo) dinka. 2. Duk lokacin da wata takadda mai mahimmaci  tazo hannunka sai kayi koka...

FASAHAR KERE-KEREN WAYAR HANNU

Image
FASAHAR KERE KERE. Assalamu alaikum, Yau InshaAllah  zamuyi tsokaci akan fasahar kere-kere. Kasancewar mu ma'abota amfani da wayar hannu, computer da makamantansu, yana dakyau mu kasance masu nazartar tare da zurfafa tunani akan waddannan abu buwa kamar haka. 1. Ya ake kera wayar yannu. 2. Yaushe aka fara kirkiri waya 3. Waye ya kirkiri waya Da sauransu. Babbar matsalar mu a yankin Africa shine rashin zurfafa bincike akan irin wadancan abubuwa,  sannan kuma gwamnatocinmu basa tallafawa harkar kerekere zaka iya  samun yara da yawa wadanda suna da basira matuka aman gwamnatocin mu basa damuwa da irin waddan nan matasa,  sunfiso a kodayaushe muzamo cima zaune saide a kera mana mu saya, wanan dalilin ne ma yasa zakaga kullum turawa saide su kiramana kaya mu siya. Idan ka dauki waya kadai zakaga kudin da kamfanoni wayoyin nan suke samu sunfi kudin da ake samu a manfetir a Nigeria. Kulum sai wani kamfani yafito da sabuwar waya mukuma sai...

VOICEMAIL (SAKON SAUTI)

Assalamu alaikum .🙏🙏🙏🙏🙏 Barakanmu da wannan lokaci🙏🙏🙏 yau InshaAllah zamuyi bayani akan voice mail (sakon sauti)🔦🔦🔦☎📟👇👇 Voicemail wata hanyace da zaka tura sakon sauti zuwa ga wanda kake nufin isar da sako.👇☎📟 Dalilan da suke sawa a tura sokon voicemail🚸 Wasu lokutan zaka iya kiran wayar wani abokin ka sai kaji ance dakai not reachable aman zaka iya tura masa voicemail, watakila kuma sakon da kake son isarwa yanada mahimmanci so sai kuma kana so ka isar da sakon akan lokaci.🙋 Idan wanda ka kirawo ya saita tsarin voicemail akan layinsa kuma kakirashi baka same shiba, kawai saika fadi sakon, idab kuna wayarsa zai ga sakon ka kuma zai saurara don sanin daliln wannan sako.👇 Amfanin voicemail 🚸👇 1.Yana temakawa wajen isarda sak...

BAKA DA BUKATAR KARYA LAYINKA NA MTN

Assalamu Alaikum. InshaAllah yau zamuyi magana akan (porting) wato yadda zaka sauya kamfanin layinka zuwa wani kamfani batare da ka canja number ba,  a kwanakin baya naga mutane da yawa suna karya layinsu na MTN sakamakon kisan yan Nigeria a kasar south Africa wanda wasu sunga hakan itace kadai hanyar dazasu huce haushin su,  to amman wannan mataki sam bai dace saboda karya layinka zai iya jawo maka asara maiyawa musamman idan kana kasuwanci kuma kwastomominka zasu dinga nemanka basu samekaba. Memakon kakarya layinka kawai ka sauya layinka daga MTN zuaa wani kamfani kamar 9mobile Golo ko Airtel,  Idan kana son ka sauya layinka daga MTN zuwa 9MOBILE ko GLO ko Airtel batareda nambarka ta sauyaba kawai sai kaje kamfanin da kake so ka koma kace musu kanason kai porting din layinka daga MTN zuwa kamfanin su, batare da wani bata lokaciba zasu saukeka daga kan MTN zuwa 9Mobile ,  ko Glo ko Airtel  idan angama nambarka bazata sauyaba aman idan zaka saka kati na kamfanin...

MATAKIN DAYAKAMATA KA DAUKA WAJEN KARE KANKA DAGA SHARIN MASU SATAR KUDI A BANKI

Assalamu Alaikum . yau InshaAllah zamuyi magana akan wata matsala da tazama ruwan dare acikin al'umma, a wannan zamani akwai wasu batagari masu amfani da wasu hanyoyi wajen sacewa mutane kudade a akaunt din su , kawai kana zaune saikaji debit alert wanda bakasan dashi ba, kuma inkaje banki sai suce da kai kaine ka ciri kudin saboda da layinka akai amfani aka cire kudin. akwai hanyoyi dayawa dasu wadannan bata gari suke bi wajen satar bayanai daga jamaa wanda mutane da dama basa kulawa ko damuwa da mahimmancin waddannan bayanai . sudai waddan mutane kulum acikin bincike suke akan yadda zasu cutar da alumma, su sun kasance suna bacci da rana da da daddarekuma sai su hau Internet suyi ta gwada sa'arsu har su dace. kadan daga cikin bayanai dasuke sata sun hada da. 1. shekarun haihuwar wanda zasu iya samu a facebook dinka ko wata social media zama su iya kiranka awaya su yaudareka da cewa su ma'aikatan bankine suna so san wasu bayanai agurinka wanda idan kai kuskure ka fa...

YADDA ZAKAYI TARaNSFAR DATA DAGA LAYINKA ZUWA WANI LAYI

YADDA ZAKA TURA DATA DAGA WANI LAYI ZUWA WANI  KO SHARING AKAN LAYIN   MTN , 9MOBILE, GLO DA AIRTEL ♨️ Assalamu alaikum barkanmu dasake saduwa a wannan dandali mai albarka yau zamuyi bayani akan yadda Zaka iya turawa yanuwanka ko abokai data daga layinka zuwa nasu kamar haka:- 🌀 YADDA ZAKAI TRANSFA   DAGA  MTN ZUWA  MTN 1. Katabbata kana da data akalla  10MB. 2. Kadanna  *131*7 # 3. Kabi umarnin dazai bayyana akan wayarka 4.. Kazabi. Pin dinka  lambobi hudu missali 1992 5. Ka danna  *131*2*1#. 6. kadanna *131*2*4*1*No. dazaka turada data.*Pin# Idab kuma sharing din data zakayi said ka  kadanna  *131*2*4*3*Pin# ko  *131*2*4*2*phone number*Pin#.   Dancire number danna *131*2*4*1* number*Pin# *131*2*4*4*Pin#. YADDA ZAKAI   TRANSFER Data DAGA   AIRTEL   ZUWA AIRTEL DON YIN TRANSFER 10MB: kadanna  *141*712*11* number wanda zaka turawa # 25MB: danna *141*712*9* number...